(ABNA24.com) Shafin yada labarai na Blumberg ya nakalto ministan cikin gida na gwamnatin hadin kan kasar Fathi Bashagha yana fadar haka a jiya Asabar.
Bashagha ya kara da ce wa gwamnatin kasar Rasha ba ta takaita wajen goyon bayan Halifa Haftar kawai ba, sai dai tana da wani shiri fiye da haka a kasar ta Libya da kuma wasu kasashen Afirka.
A ranar 13 ga watan Fabrairu da muke ciki ne sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bada sanarwan cewa gwamnatin kasarsa tana shirin sauya tsarin samuwar sojojinta a nahiyar Afrika, wanda kuma zai hada da rage yawan sojojinta a yankin Sahel na yammacin Afirka.
A halin yanzu dai Amurka tana da sojoji 6000 a nahiyar Afirka. Tana da sojoji 800 a yammacin Afirka, sannan 500 a kasar Somalia. Sai kuma wasu wadanda ba’a bayyana adadinsu ba a arewacin kasar Niger.
/129
24 Faburairu 2020 - 05:10
Lambar labari: 1012708
Gwamnatin hadin kan kasa ta kasar Libya ta bukaci Amurka ta kafa sansanin sojojinta a cikin kasar don hada kasar Rasha samun karfi a cikinta.